A ran 5 ga wata, a Libreville, babban birnin kasar Gabon, shugaban majalisar dokokin kasar Guy Nzouba-Ndama ya bayyana cewa, hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka yana kawo cin moriyar juna, kuma bangarori daban daban za su samu sakamakon daga wannan aiki.
Bayan Guy Nzouba-Ndama ya halarci bikin nune-nune sakamakon da aka samu daga dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka wadda ofishin jakadanci kasar Sin da ke kasar Gabon ya shirya, ya bayyana cewa, bisa hadin gwiwa da suke yi, kasashen Afirka suna iya gano kyakkyawar makoma a fannin dangantakar hadin gwiwa a tsakanin bangarori biyu. Guy Nzouba-Ndama ya bayyana cewa, bayan shirya dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka a birnin Beijing, an samun babban sakamako a fannin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka musamman ma kasar Gabon, an iya gano kyakkyawar makoma.
A ran 8 ga wata, a birnin Sharm El Sheikh, a madadin shugaban kasar Gabon Ali-Ben Bongo Ondimba, Guy Nzouba-Ndama zai halarci taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kai tsakanin Sin da Afirka.(Abubakar)
|