Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 15:00:24    
Shugaban kasar Senegal ya yanke kyallen bude ma'aikatar hada hadar motocin da kasar Sin ta kafa a kasar

cri
A ran 4 ga wata, a birnin Thies da ke arewacin kasar Senegal, shugaban kasar Abdoulaye Wade ya yanke kyallen domin fara aikin ma'aikatar hada hadar motocin da kasar Sin ta kafa a kasar.

Da farkon, Abdoulaye Wade ya nuna babban yabo ga ingancin motocin kasar Sin, daga baya, ya yanke kyallen fara aikin sashen hada hadar motocin kasar Sin da aka kafa a kamfanin harhada motoci na kasar Senegal, kuma ya kai ziyarar gani da ido a sashen hada hadar motoci tare da jami'an gwamnatin.

A cikin jawabin da Abdoulaye Wade ya yi, ya sake nuna babban yabo ga kyakkyawar dangantakar hada kai a tsakanin kasashen biyu. Ya ce, gwamnatin kasar Sin ta samar da rancen kudi yuan miliyan 160 ga gwamnatin Senegal cikin sauri don nuna goyon baya ga shirin na sabunta fasahin motar bos da kasar Senegal ta tsara, wannan ya shaida cewar kasar Sin tana yin kokari wajen nuna goyon baya ga bunkasuwar kasar Senegal. Abdoulaye Wade ya bayyana godiya ga kokarin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi wajen aiwatar da ayyukan ba da taimako ga kasar Senegal.(Abubakar)