Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 14:29:03    
Matakin tallafin tattalin arziki da kasar Sin ta dauka ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar

cri

A kwanan baya, yayin da yake hira da manema labaru, mataimakin shugaban asusun ba da lamuni na duniya wato IMF Takatoshi Kato ya bayyana cewa, matakin tallafin tattalin arziki da kasar Sin ta dauka ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar.

Bugu da kari, Malam Takatoshi Kato ya furta cewa, a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, bayan abkuwar matsalar kudi, gwamnatin Sin ta kaddamar da shirin tallafin tattalin arzikin kasar da sauri. Yana mai ra'ayin cewa, abubuwan da aka tanada a cikin shirin tallafin tattalin arziki da Sin ta tsara ya zama kyakkyawan abin koyi ga kasa da kasa.

Malam Takatoshi Kato ya kara da cewa, Sin ta riga ta samu ci gaba a fannoni da dama kamar su farashin kudin RMB da kasuwar hannayen jari da dai sauransu, kuma ya yi imani da cewa, Sin za ta ci gaba da yin kwaskwarima a kasar.

Dadin dadawa, malam Takatoshi Kato ya nuna cewa, kasar Sin muhhimiyar mamba ce ta kungiyar G20, kuma za ta taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya.(Asabe)