
Wakilinmu ya ruwaito mana labarin dake cewa, saboda halin yaduwar cutar murar A(H1N1) da duniya ke ciki ya kara tsananta, kasashe daban-daban sun kara sa ido kan batun, kuma sun dauki matakan yin allurar rigakafin cutar.
An habarta cewa, a ran 2 ga wata kasar Isra'ila ta fara kaddamar da shirin yin amfanin da allurar rigakafin, sabo da haka, daga ran 4 ga wata, hukumomin kula da lafiya za su yi wa mutanen da suke da shekaru 5 zuwa 65 a duniya allurar. Amma, jama'a bu su himmatu ga yin allurar ba, bisa binciken da aka yi, yawan mutanen Isra'ila da ba su son yin allurar ya kai kimanin kashi 47 bisa 100. Saboda haka, hukumar kiwon lafiya ta kasar tana shirin fadakar da kan jama'a.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Austriya ya bayar, an ce, hukumar kiwon lafiya ta kasar ta yi shirin yi wa jama'arta allurar daga ran 9 ga wata, kuma jihohi da dama sun fara yin aikin share fage domin yin allurar ga yara da tsofoffi da kuma mata masu juna biyu da makamatansu wadanda suka fi kamuwa da cutar.(Amina)
|