Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 09:29:42    
Hukumar baitumali ta kasar Amurka ta sanar da cewa ci gabada yawan kudin ruwa na asusun tarrayar Amurka ba zai canja ba

cri

A ran 4 ga wata, hukumar baitumali ta kasar Amurka ta sanar da cewa, yawan kudin ruwa na asusun tarrayar Amurka zai a ci gaba da kasancewar a matsayin sifiri zuwa 0.25 bisa dari, don sa kaimi ga farfado da tattalin arziki na kasar. Kuma wannan kuduri ya dace da hasashen da aka yi kan kasuwani.

Bayan da aka kammala taron da aka saba yi kan manufar kudi a ran nan, kwamitin FOMC na hukumar baitumali ta Amurka ta bayar da sanarwa cewa, tattalin arzikin kasar ta ci gaba da farfadowa, halin da kasuwannin kasar ke ciki bai canja ba, kuma kasuwar gidaje da filaye ta samu bunkasuwa a cikin 'yan watanni da suka wuce, kuma yawan kudin da jama'ar kasar suka kashe ya karu. Ko da yake tattalin arzikin ba zai samu bunkasuwa sosai ba a cikin wani lokaci, amma kwamitin ya yi hasashen cewa, matakan da aka dauka na daidaita kasuwar kudi da hukumomin kudi da manufofin kara kasafin kudi da karfin kasuwanni za su sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Amurka.(Abubakar)