A ran 3 ga wata, wani jami'in yankin Puntland dake arewa maso gabashin kasar Somaliya ya bayyana cewa, 'yan sanda na yankin sun murkushe wata makarkashiyar fashin wani jirgin sama bisa taimakon ma'aikatan jirgin da fasinjojin dake a jirgin, sun kama mutane 2 da ake tuhumar su da hannu a laifin.
Gwamnan jihar Bari dake yankin Puntland Muse Gele ya bayyana a wajen taron manema labaru cewa, a filin jiragen sama na birnin Bossaso na kasar Somaliya, mutane 2 sun shiga wani jirgin sama da ya tashi zuwa kasar Djibouti dauke da bindigogi. Yayin da jirgin yake tafiya, mutanen biyu sun kutsa kansu cikin dakin matukin jirgin da yunkurin mai da jirgin ta nufi zuwa wurin 'yan fashin teku wato garin Las Qoray dake yammacin yankin Puntland, amma ma'aikatan jirgin da fasinjoji sun ci karfinsu, jirgin ya koma filin jiragen sama na Bossaso a karshe. Daga baya, 'yan sanda sun kama mutanen biyu.
Mr Gele ya furta cewa, nufin mutanen biyu shi ne yin garkuwa da 'yan jarida 2 daga kasar Jamus dake cikin jirgin don yin amfani da su wajen yin musayar 'yan fashin tekun Somaliya da sojojin ruwa na kungiyar tsaron NATO suka kama a tekun Indiya da haddin ruwa na mashigin tekun Aden a kwanakin baya.(Zainab)
|