Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 09:08:03    
Hadarin ruwa da ya abku a kogin dake tsakanin kasashe Nijeriya da Benin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 40

cri
Yawan mutanen da suka rasu a sakamakon wani hadarin ruwa da ya abku a kogin dake tsakanin kasashe Nijeriya da Benin ya karu zuwa 40, ban da wannan kuma, akwai mutane 15 da ba a san ina suke ba a yanzu.

Wani jami'I a jihar Kwara ta Nijeriya dake dab da wurin abkuwar hadarin ya shedawa manema labaru cewa, ya zuwa ran 3 ga wata da sassafe, an debo gawawwaki 40 daga kogin, amma akwai mutane 15 da ba a san ina suke ba a yanzu.

An labarta cewa, jiragen ruwa na fasinja 2 dake dauke da fasinjoji fiye da 80 tare da wasu ma'aikatansu sun nutse cikin kogin yayin da suka kan hanyar zuwa Nijeriya daga Benin. Bayan abkuwar hadarin, an yi aikin ceto cikin gaggawa, a sakamakon haka mutane 35 sun tsira da ransu.

Wani jami'in jihar Kwara ya furta cewa, wannan hadari ya fi tsanani a cikin wadanda suka abku a wannan yanki. Dadin dadawa, ana ci gaba da aiwatar da ayyukan ceto.(Amina)