Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 18:03:55    
Akasarin kasashe masu tasowa sun yi kira da kada a ki amincewa da 'Takardar bayani ta Kyoto'

cri

An bude taron shawarwari a karo na 5 kan sauyawar yanayi na MDD na shekarar 2009 a ran 2 ga wata a birnin Barcelone na kasar Spaniya. A bikin bude taron, akasarin kasashe masu tasowa sun yi kira ga kasashe masu sukuni da kada su ki amincewa da 'Takardar bayani ta Kyoto', kasashe masu tasowa sun jaddada cewa, babban aikin da ke gaba shi ne, tabbatar da nauyin da ke kan kasashe masu sukuni dangane da wa'adi na biyu na yin alkawarin rage fitar da gurbataccen hayaki.

Shugaban tawagar kasar Sudan ya yi wani jawabi a madadin rukunin G77 da kasar Sin cewa, kasashe masu sukuni suna yunkurin kawo karshen yin wasarere da 'Takardar bayani ta Kyoto', wannan ya sabawa ka'idar daukar nauyi daban daban da ke kan ko waccensu, ta yadda za a kawo babban kalubale ga babban taro na sauyawar yanayi na MDD da za a yi a birnin Copenhagen.

Wani wakilin gamayyar kasashen kananan tsibirai wato AOSIS ta nuna goyon baya ga matsayin G77 da kasar Sin. Haka kuma wakilan kasashen Afirka suna ganin cewa, tilas ne a gaggauta yunkurin shawarwari, tilas ne kasashe masu sukuni su tsara wani shiri na rage fitar da gurbataccen hayaki cikin sauri.(Danladi)