A ran 30 ga wata, kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta bayar da sabon rahoto kan yanayin cutar AH1N1 na duniya. Rahoton ya ce, a makon da ya gabata, yawan mutanen da suka mutu a arewacin nahiyar Amurka a sakamakon kamuwa da murar AH1N1 ya kai 636, wanda ya fi yawa tun daga watan Afrilu na wannan shekara da cutar AH1N1 ta barke.
Rahoton ya kara da cewa, ya zuwa ran 25 ga wata, yawan mutanen da aka tabbatar da kamuwa da murar AH1N1 a dakunan gwaje-gwaje na duk duniya ya kai dubu 440, yawa mutanen da suka mutu ya kai 5700. Amma wasu kasashe ba su sa lura sosai kan cutar, sabo da haka, yawan mutanen da suka kamu da murar ya fi adadin da rahoton ya bayar yawa.
A ran nan kuma, kungiyar WHO ta bayar da sanarwa, inda ta jaddada cewa, sa allurar rigakafin cutar AH1N1 bisa abin da aka kayyade ba zai halaka mutane ba. Amma sanarwar ta kuma jaddada cewa, za a ci gaba da dudduba cikas da allurar rigakafin cutar AH1N1 ta kawo wa mutane.(Lami)
|