Ran 29 zuwa ran 30 ga wata, tawagar gwamnatin kasar Sin ta fuskar al'adu da ke karkashin shugabancin Cai Wu, ministan al'adu na kasar Sin ta kai wa kasar Seychelles ziyara a hukumance, bisa gayyatar da Vincent Meriton, ministan kula da bunkasa unguwanni da al'adu da wasannin motsa jiki da harkokin matasa na Seychelles ya yi.
A rakiyar Wang Weiguo, jakadan kasar Sin a Seychelles, tawagar Sin ta fuskar al'adu ta gai da James Michel, shugaban Seychelles, kuma ta yi shawarwari tare da Mr. Meriton, inda bangarorin 2 suka darajta dangantaka a tsakanin kasashen 2 a harkokin al'adu, kuma sun bayyana fatansu na ci gaba da inganta yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsu a harkokin al'adu.
Wannan ziyara wani bangare ne na harkar "mai da hankali kan kasar Sin ta fuskar al'adu a shekarar 2009" da kasar Sin ta shirya a kasashe fiye da 20 na Afirka daga watan Afrilu zuwa na Nuwamba a bana.(Tasallah)
|