Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 20:25:18    
Kungiyar AU ta yanke shawarar kakabawa gwamnatin soja ta kasar Guinea takunkumi

cri

Ran 29 ga wata a Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar gamayar kasashen Afirka, wato AU ya yanke shawarar kakabawa gwamnatin soja ta kasar Guinea takunkumi, ana hana jagora Moussa Dadis Camara wanda ya shugabanci juyin mulki da mabiyansa da su kai ziyara a ketare kuma an hana su taba dukkan dukiyoyinsu.

A wannan rana, kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar AU ya yi taro a birnin Abuja. Bayan taron, an bayar da sanarwa cewa, kwamitin zai hada kansa da kungiyar ECOWAS domin daukar matakan da ake bukata don kakabawa gwamnatin soja ta kasar Guinea takunkumin, hana ba da Visa ga Camara da mabiyansa, kuma za a hana su kai ziyara a ketare tare da hana su amfani da dukkan dukiyoyinsu.

Ban da haka kuma, a wannan rana, wannan kwamiti ya yanke shawarar takunkumin haramta sayarwa kasar Guinea makamai, kuma ya sake yin Allah wadai da kisan gillar da aka yiwa fararen hula 150 a ran 28 ga watan Satumba a Conakry, babban birnin kasar Guinea. [Musa Guo]