Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 15:22:36    
An rufe taron kwamitin musamman kula da sauye-sauyen yanayi a tsakanin gwamnatoci na Majalisar Dinkin Duniya wato IPCC a karo na 31

cri
A ran 29 ga wata a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, an rufe taron kwamitin musamman na kula da sauye-sauyen yanayi a tsakanin gwamnatoci na Majalisar Dinkin Duniya wato IPCC a karo na 31. A yayin taron, an tabbatar da tsarin rahoton kimantawa da rukuni daban daban da kwamitin ya yi a karo na biyar, da lokacin da za a zartas da rahoton kimantawa a karo na biyar.

Bisa kudurin da aka tsara a yayin taron, an ce, lokacin da za a zartas da rahoton kimantawa na rukuni na farko da na biyu da kuma na uku na IPCC da rahoton kimantawa da za a yi a karo na biyar shi ne watan Satumba na shekarar 2013, da watan Maris na shekarar 2014, da kuma watan Afrilu na shekarar 2014, kana da watan Satumba na shekarar 2014.

Yayin da yake hira da wakilinmu, Malam Shen Xiaonong, mataimakin shugaban hukumar kula da yanayi ta kasar Sin dake jagorar tawagar kasar Sin don halartar taron ya bayyana cewa, a cikin rahoton kimantawa a karo na biyar, da akwai abubuwa biyu dake jawo hankalin jama'a, wato za a mai da hankali kan sauye-sauyen yanayi a yankuna, da kara kimanta tasirin da sauyin yanayi ya kawo wa tattalin arziki da zaman al'umma.(Asabe)