A ran 29 ga wata, shugaban Cameroon Paul Biya da takwaran aikinsa na Chadi Idriss Deby dake ziyara a kasar sun ba da wata hadaddiyar sanarwa cewa, kasashen biyu za su dauki matsayi daya a lokacin taron yanayi na Copenhagen, a kokarin yin kira ga kasa da kasa da su mai da hankali kan matsalar fari a shiyyar tabkin Chadi, da jaddada ba da kudin agaji ga tsarin halittu a wannan shiyya.
Bayan haka, sanarwar ta ce, kasashen biyu za su kara hada gwiwa, domin yaki da cinikayyar makamai ba bisa doka ba a yankin iyakacin kasa, da fashi a kan hanyoyi, da kuma saukaka takardar izni ta musanyar mutane da kayayyaki tsakaninsu.
A ran 29 ga wata, a filin jirgin sama, bayan da ya kammala ziyara a kasar Cameroon, Idriss Deby ya furta cewa, rikice-rikice a tsakiyar nahiyar Afirka suna ci gaba da kasancewa. Duk da haka, sabon yanayin da ake ciki a fannin siyasa zai taimakawa kasashe membobin kungiyar ECCAS a fannin samun bunkasuwa baki daya tare da sauran kasashen Afirka.(Fatima)
|