Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 09:20:24    
Gwamnatin kasar Afrika ta kudu za ta dauki sabon matakin yaki da cutar AIDS

cri
A ran 29 ga wata, a Cape Town, babban birnin kasar Afrika ta kudu, shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta dauki matakin yaki da tabarbarewar annobar cutar AIDS.

Malam Jacob Zuma ya furta cewa, a ran 1 ga watan Disamba na bana wato ranar yaki da cutar AIDS ta duniya, gwamnatin kasar za ta sanar da sabon matakin yaki da cutar AIDS don rage yawan mutuwar matasan da suka kamu da cutar. A sa'i daya kuma, ya yi kira ga jama'ar kasar da su hada kai don yaki da cutar. Amma malam Jacob Zuma bai fayyace takamaimen matakin yaki da cutar da gwamnatin za ta dauka ba.(Asabe)