Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-29 14:40:37    
Hukumar WHO za ta samar da allurar rigakafin cutar A(H1N1) miliyan 200 ga kasashe masu tasowa

cri
A ran 28 ga wata, malama Margaret Chan, babbar darektar hukumar kiwon lafiya wato WHO ta bayyana cewa, a cikin watanni 12 masu zuwa, hukumar za ta samar da allurar rigakafin cutar A(H1N1) miliyan 200 ga kasashe masu tasowa don yaki da karuwar annobar cutar A(H1N1).

Malama Margaret Chan ta yi wannan alkawari ne a gun taron manema labarun da aka yi a birnin Havana. Ta furta cewa, duk da babu isashen karfin harhada allurar rigakafin cutar A(H1N1) a duk duniya, amma hukumar ta rigaya ta yi mu'amala da kasashe da kamfanonin dake da karfin harhada allura ta M.D.D., ta yadda za a samu wasu allura ba tare da biyan kudi ba. Hukumar WHO za ta samar da wadannan allura ga kasashe masu tasowa fiye da dari daya.(Asabe)