|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-10-29 09:15:43
|
Nijeriya ta yarda da yi amfani da kudin asusu mai dimbin yawa domin bunkasa Niger Delta
cri
Wakilinmu ya ruwaito mana labari cewa, a ran 28 ga wata, shugaban Nijeriya Mr Umaru Yar'dua ya yarda da ya yi amfani da kudin asusun tarayyar gwamantin kasar kamar dala biliyan 1.34 domin bunkasa manyan ayyuka da sauransu a yankin Niger Delta wanda ya fi samar da man fetur.
Ministar sadarwa ta Nijeriya Madam Dora Akunyili ta bayyana cewa, kudin nan zai taimaka ga ayyukan 45 dake kunshe da ayyukan kafa hanyoyi da gadoji da asibitoci da kuma makarantu da makamatansu, ko shakka babu, wadannan ayyuka za su kara kaimi domin yunkurin bunkasa yankin. Bisa labarin da aka bayar, an ce, kudin da za a yi amfani da shi zai fito daga shirin raya tattalin arziki kamar dala biliyan 2 da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta gabatar a farkon wata nan.(amina)
|
|
|