A ran 27 ga wata a fadar shugaba, shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade ya baiwa jakadan Sin dake a kasar Lu Shaye lambar yabo ta kasar Senegal don nuna yabo gare shi da ya ba da gudummawa wajen raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Senegal.
A yayin bikin bayar da lambar yabo, Mr Wade ya furta cewa, gwamnatin Senegal ta nuna babban yabo ga dangantakar hadin gwiwa tsakanin Sin da Senegal a fannoni daban daban, an sheda dukkan ayyukan da kasar Sin ta gudanar a kasar Senegal, gwamnatin Senegal da jama'arta sun nuna godiya game da wannan.
Karamin jakadan Sin na sashen kula da harkokin cinikayya na ofishin jadakan Sin dake a kasar Senegal Zhou Zhaoming ya bayyana cewa, tun bayan da aka sake kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Senegal a ran 25 ga watan Oktoba na shekarar 2005, bangarorin biyu sun gudanar da ayyukan hadin gwiwa da aka tabbatar a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kana ana gudanar da yawancin manyan ayyukan ba da taimako ga kasar Senegal.(Zainab)
|