|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2009-10-28 14:38:36
|
 |
An yi ganawa tsakanin ministocin harkokin waje na kasashen Sin da Indiya da Rasha
cri
A ran 27 ga wata a birnin Bangalore na Indiya, ministocin harkokin waje na kasashe Sin da Indiya da Rasha sun yi ganawa tsakaninsu, kuma sun ba da sanarwa cikin hadin kai.
Sanarwa ta ce, ministocin 3 sun tattauna kan yadda za a kara yin hadin kai tsakanin kasashensu a duk fannoni, domin amfanawa jama'arsu ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankuna.
Kasashen uku sun dora babban muhimmanci kan batun sauyawar yanayi, kuma suna fatan kasashen daban-daban za su kara yin hadin kai da kuma taka rawa wajen yaki da batun sauyawar yanayi.
Dadin dadawa, sanarwa ta ce, mai yiwuwa ne, kasashen 3 sun taimakawa juna a fannin makamashi, kuma za su kara bunkasa dangantaka a tsakanin kasashen 3 ta hanyar kafa dangantakar kawo moriyar juna.
Ministocin 3 sun jaddada a sanarwar cewa, kamata ya yi, a kyautata tsarin MDD da zummar yaki da matsalolin duniya daban-daban. Ban da wannan kuma, sanarwa ta nuna damuwa ga halin zaman lafiya da Afghanistan ke ciki, kuma ta yi maraba da ganawa da wakilan kasashe 6 wato Sin da Amurka da Rasha da Britaniya da Faransa da Jamus da kuma wakilan kungiyar EU da Iran suka yi a kwanan baya a Geneva, bugu da kari ta nanata cewa, kamata ya yi a yi yunkurin shawo kan matsalar Iran ta hanyar siyasa da diplomasiyya.(amina)
|
|
|