A ran 27 ga wata, hukumar NASA ta Amurka ta bayyana cewa, saboda dalilan yanayi, an dage lokacin harbi roka mai lambar "Ares I-X" zuwa ran 28 ga wata, wanda aka tsai da kudurin yinsa a wannan rana.
"Ares I-X" shi ne modal din sabbin rokoki masu daukar kayayyaki masu lambar Ares. An labarta cewa, rokoki masu lambar Ares da kumbo mai sunan "Orion" da kumbo mai saukar wata mai suna "Altair" su ne manyan matakai 3 na sabon shirin ganowa sararin samaniya.(amina)
|