A watan Oktoba, an fara yin allurar rigakafin cutar murar A (H1N1) a kasashen Amurka da Japan da Faransa da kuma Ingila. Tare da kasashen Jamus da Canada sun sanar da yin allurar a ran 26 ga wata da kasar Koriya ta kudu ta sanar da yin allurar a ran 27 ga wata, an yi tashen yin allurar rigakafin cutar murar A (H1N1) a duniya.
Bisa halin da ake ciki a kasashe daban daban, an kiyasta cewa, a makonni biyu masu zuwa, za a fara yin allurar rigakafin cutar murar A (H1N1) a kasashen Turai da yawa kamar kasar Spain. Ban da wannan, wasu kasashe masu tasowa na nahiyar Asiya da ta Afirka da ta Latin Amurka sun riga sun mika wa hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO rokon samun allurar rigakafin cutar murar A (H1N1) nan da nan.(Zainab)
|