Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-28 09:20:00    
'Yan fashin tekun Somaliya sun sace wani jirgin ruwan kasar Ingila mai daukar fasinjoji

cri
Kakakin ma'aikatar sadarwa ta kasar Somaliya Sheikh Abdirisaq Mohamed Qaylow ya bayyana cewa a ran 27 ga wata, 'yan fashin tekun Somaliya sun sace wani jirgin ruwan kasar Ingila mai daukar wani dan kasar Ingila da matarsa a tekun Indiya.

Mr Abdirisaq ya furta cewa, gwamnatin Somaliya ta riga ta samu sako dangane da mutanen biyu, 'yan fashin tekun Somaliya sun yi garkuwa da su yayin da suke tashi zuwa kasar Tanzania, yanzu dai gwamnatin Somaliya tana neman inda mutanen dake cikin jirgin ruwan suke yanzu.

Wannan jirgin ruwa ya bace a ran 23 ga wata yayin da yake tashi daga kasar Seychelles zuwa kasar Tanzania, jirgin ya taba bayar da sakon neman taimako, daga baya ya bace. Har zuwa ran 27 ga wata, kungiyar ba da gudummawa kan teku ta samu sakon.

Mutanen biyu dake cikin jirgin su ne Paul Chandler mai shekaru 58 da matarsa Rachel Chandler mai shekaru 55. Bisa labarin da aka bayar, an ce, sojojin ruwan kasar Ingila sun riga sun tura jiragen ruwan yaki 2 don nemansu a tekun da lamarin ya faru.(Zainab)