Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-27 21:21:15    
Reshen kungiyar Al-Qaeda dake kasar Iraki ya dauki alhakin jerin hare-haren boma-bomai na birnin Bagadaza

cri

A ran 26 ga wata, wani reshen kungiyar Al-Qaeda dake kasar Iraki ya bayar da sanarwa ta Internet cewa, ya dauki alhakin kai jerin hare-haren boma-bomai da suka faru a ran 25 ga wata a birnin Bagadaza.

Wata kungiya mai suna "The Islamic State of Iraq" wato ISI ta sanar a ran 26 ga wata cewa, membobinta sun kai hare-haren kunar bakin wake ga ma'aikatar shari'a ta kasar Iraki da ginin gwamnatin jihar Bagadaza.

A ran 25 ga wata, an kai hare-haren boma-boman kunar bakin wake da aka dasa cikin mota a ma'aikatar shari'a ta kasar Iraki da ginin gwamnatin jihar Bagadaza a lokaci daya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 155, kuma mutane fiye da 500 suka ji rauni. Firaministan kasar Iraki Nuri al-maliki ya nuna a ran 25 ga wata cewa, bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, wadanda suka kai hare-haren su ne kuma mutanen da suka kai farmakin boma-bomai a ran 19 ga watan Agusta, suna karkashin jagorancin jam'iyyar farfadowar zaman al'ummar ta Arabiya da kungiyar Al-Qaeda.(Lami)