 A ran 26 ga wata da yamma, ma'aikatar kula da harkokin zirga-zirga ta kasar Nijeriya da kamfanin ayyukan gine-gine na kasar Sin wato CCECC sun daddale yarjejeniya dangane da karin bayani kan gina hanyoyin jiragen kasa a tsakanin Abuja da Kaduna, wannan al'amari ya faru ne a Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, abin da ya bayyana cewa, kasar Nijeirya ta sake fara gudanar da aikin gina hanyoyin jiragen kasa da aka tsayar a tsawon fiye da shekara daya.
Mataimakin babban manajan kamfanin CCECC Zhou Tianxiang da ministan kula da harkokin zirga-zirga na kasar Nijeriya su ne suka sa hannu kan yarjejeniyar da shafi karin bayani a madadin bangarorin Sin da Nijeriya. Zhou Tianxiang ya bayyana cewa, tsawon hanyoyin jiragen kasa a tsakanin Abuja da Kaduna ya kai kilomita 186.5, yawan kudin da aka tanada a yarjejeniyar ya kai dala miliyan 850, kana wa'adin yarjejeniyar ya kai tsawon watanni 36.(Zainab)
|