Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-26 10:15:45    
Kasa da kasa sun yi Allah wadai da hare-haren boma-boman da aka kai a kasar Iraki

cri
A ran 25 ga wata a cibiyar birnin Baghdad na kasar Iraki, an kai hare-haren boma-bomai na kunar bakin wake da aka dasa cikin mota, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 147, kuma mutane kimanin dari 6 sun ji rauni. A wannan rana, kasa da kasa sun yi Allah wadai da abkuwar lamarin.

Kwamitin sulhu na MDD ya bayar da wata sanarwa, inda ya yi Allah wadai da abkuwar wannan mummunan lamarin hare-haren sosai. Sanarwar ta ce, kwamitin ya nuna juyayi ga iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon kai hare-haren, kuma ya jaddada cewa, zai nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Iraki da jama'arta, da yin kokari wajen cika alkawarin tabbatar da tsaro a kasar Iraki. Sanarwar ta jaddada wajibcin gurfanar da masu kai hare-haren da masu shirya aikin da masu ba da kudin taimako a gaban kotu, kuma ya yi kira ga dukkan kasashe membobin MDD da su ba da gudummawa ga kasar Iraki wajen daukar matakan warware matsalar bisa kiyaye dokokin duniya da sharudan da aka tanada a kudurin kwamitin sulhun.

Kazalika babban sakataren MDD Ban Ki-moon da kungiyar LAS da kasar Sweden da ke jagorancin kungiyar EU a wanna zagaye da shugaban kasar Amurka Barack Obama da kuma shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy sun yi Allah wadai da abkuwar lamarin a wannan rana.(Zainab)