Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-26 09:26:12    
An sheda fashewar boma-bomai a birnin Baghdad

cri

A ran 25 ga wata a birnin Baghdad na kasar Iraki, an kai hare-haren kunar bakin wake ta hanyar ta da boma-bomai da aka dasa cikin mota, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 147, kuma mutane 721 suka ji rauni. Kungiyar kawancen kasashen Larabawa ta LAS da kungiyar EU sun bayar da sanarwar yin Allah wadai da abkuwar lamarin kai hare-haren boma-boman.

Da karfe 10 da rabi na ranar 25 ga wata, an kai hare-haren boma-bomai da aka dasa cikin mota a gaban babban ginin gwamnatin jihar Baghdad da otel din Mosul. Bayan dakikoki 10, an kai wani harin boma-bomai na daban ga babban ginin ma'aikatar shari'a ta kasar Iraki. Ma'aikatan shari'a 35 da na majalisar dokokin jihar Baghdad 25 ne suka mutu a sakamakon hare-haren.

Ofishin firayin ministan kasar Iraki ya bayar da wata sanarwa a wannan rana, inda ya furta cewa, masu kai hare-haren sun yi yunkurin tada tarzoma, da kawo cikas ne ga harkokin siyasa na kasar da zaben majalisar dokoki da za a yi a watan Janairu na badi.

Ya zuwa yanzu dai, babu wata kungiya ko wani mutum da ya daukin alhakin kai hare-haren. Wani jami'in gwamnatin Baghdad ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne kungiyar ta'addanci dake a yankin da membobin jam'iyyar Ba'ath ta Larabawa da aka haramta su ne suka kai hare-haren.(Zainab)