Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-22 20:21:33    
Kungiyar AU ta shirya taron shugabanni na musamman kan matsalar 'yan gudun hijira

cri

A ran 22 ga wata a birnin Kampala, babban birnin kasar Uganda, kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU ta shirya taron shugabanni na musamman kan matsalar 'yan gudun hijira, babban take na wannan taro shi ne, 'kungiyar AU tana tinkarar kalubale daga matsalar 'yan gudun hijira'.

A bikin bude taron, babban kwamishina mai kula da harkokin 'yan gudun hijira na MDD Antonio Guterres ya yi wani jawabi a madadin babban sakatare Ban Ki-Moon. Mr. Guterres ya ce, matsalar 'yan gudun hijira wata babbar matsala ce a nahiyar Afirka, kira wannan taron shugabanni na musamman ya bayyana burin siyasa da aniyar kasashen Afirka wajen daidaita wannan matsala.

Shugaban kwamitin kungiyar AU Jean Ping ya fadi cewa, 'yan gudun hijira masu yawa a nahiyar Afirka sun samu ne sakamakon tabarbarewar yanayin hallitu, amma wani babban dalili shi ne, mutane ne su kan haddasa wannan matsala.

Bisa kididdigar kungiyar AU, an ce, akwai 'yan gudun hijira fiye da miliyan 17 a Afirka, sakamakon yaki, da rikici, da yunwa, da lalacewar hallitu da dai sauransu.(Danladi)