Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-22 09:19:46    
Yawan kudin da aka samu daga kayayyakin masana'antu na kasar Zimbabwe ya karu da ninki biyu a farkon rabin shekarar bana

cri
Bisa rahoton kididdigar da kungiyar hadin kan masana'antu ta kasar Zimbabwe ta bayar a ran 21 ga wata, an ce, yawan kudin da aka samu daga kayayyakin masana'antu na kasar Zimbabwe ya karu da ninki biyu a farkon rabin shekarar bana.

Rahoton ya ce, tun da aka kafa hadaddiyar gwamnatin kasar Zimbabwe a watan Fabrairu na bana, yawan masana'antun kasar da suka farfado da aiki ya karu daga kashi 10 cikin dari zuwa kashi 32.3 cikin dari. Sakamakon haka, yawan kudin da aka samu daga kayayyakin masana'antu na kasar Zimbabwe ya karu da kashi 110 cikin dari a farkon rabin shekarar bana.

Ban da haka kuma, rahoton ya kara da cewa, kafuwar hadaddiyar gwamnatin kasar ya kara samun imani ga masana'antu da cinikayya. Ya zuwa yanzu, an riga an zuba jari kimanin dala biliyan 1.5 kan sana'ar kera kayayyaki, kuma an yi amfani da galibin yawansa a fannin sake samar da wutar lantarki a tashoshin samar da lantarki, da kara karfin janareta na tashoshin samar da lantarki.(Asabe)