Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-21 11:24:57    
Sin ta riga ta soke yawan basussuka 150 da take bin kasashen Afirka 32

cri

A ran 20 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake a MDD Liu Zhenmin ya bayyana cewa, ya zuwa watanni 3 na farkon shekarar da muke ciki, kasar Sin ta riga ta soke yawan basussuka 150 da take bin kasashen Afirka 32.

Liu Zhenmin ya bayyana hakan ne yayin da yake yin jawabi kan batun Afirka a gun babban taron MDD a karo na 64 da aka gudanar a wannan rana. Ya ce, bayan abkuwar rikicin hada-hadar kudi na duniya, Sin ta warware matsalolinsu, da ci gaba da ba da gudummawa iri daban daban ga kasashen Afirka, ciki har da taimako ba tare da biyan kudi ba, da ba da rancen kudi ba tare da ruwan kudi ba, da kuma ba da rance mai gatanci. Sin ta dora muhimmanci kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannonin inganta aikin noma da gina ayyukan yau da kullum da horar da gwanaye da kuma na kiwon lafiya, wadannan sun fi muhimmanci a cikin shirin Afirka kan bunkasa sabbin abokai.

Ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa ga kasashen Afirka a fannonin aikin noma, da ba da ilmi, da kiwon lafiya, da makamashi masu tsabta da dai sauransu, kuma za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasashen Afirka da su yi kokari wajen warware rikice-rikice da shimfida zaman lafiya.

Liu Zhenmin ya furta cewa, don cimma shirin Afirka kan bunkasa sabbin abokai, kamata ya yi kasashen duniya su dora muhimmanci kan wadannnan abubuwa a kasa, wato ya kamata a cika alkawarin ba da gudummawa tun da wuri, da kara samar da jari, da girmamawa ikon mallakar kasashen Afirka, da inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da ba da taimako ga kasashen Afirka wajen raya kasa, da kuma inganta amfanin hukumomin duniya.(Zainab)