Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-19 09:33:57    
Kasar Sin babbar bakuwa ta bikin nunin littattafai ta Frankfurt ta kawo karshen ayyukanta

cri

A ran 18 ga wata a dakin nunin littattafai na Sin a Jamus, kasar Sin babbar bakuwa a gun bikin nunin littattafai ta kasa da kasa ta Frankfurt ta 61 na 2009 ta mikawa kasar Argentina takardar zama babbar bakuwa saboda Argentina za ta zama babbar bakuwa ta bikin a shekarar 2010. Wannan ya bayyana cewa, an kawo karshen ayyukan kasar Sin a matsayin babbar bakuwa na tsawon shekarar 1 na bikin.

Bayan da aka kammala bikin, mataimakin shugaban hukumar dab'in littattafai ta Sin Mr Wu Shulin ya furta cewa, A kan matsayin babbar bakuwa na tsawon shekarar 1, kasar Sin ta cimma nasara wajen yin ayyukan mu'amalar al'adu 612. Bugu da kari, a fannin cinikayyar ikon dab'in littattafai, yawan ikon dab'in littattafai da kasar Sin ta fitar ya kai 2417 wanda ya kai matsayi ne na daya na tarihin bikin.Shugabar kwamitin share fage na Argentina a matsayin babbar bakuwa a bikin baje kolin littattafai na Frankfurt kuma mataimakiyar sakatariyar al'adu ta Argentina Madam Magdalena Faillace ta karbi takardar zama babbar bakuwa daga wajen Wu Shulin. Kuma ta fadi cewa, za ta koyi darasi daga kasar Sin domin cimma nasara wajen gudanar da ayyuka a matsayin babbar bakuwa ta bikin Frankfurt a shekarar badi.(amina)