A ran 16 ga wata, kungiyar dakaru mafi girma ta kasar Nijeriya wato MEND ta bayar da sanarwar cewa, a ran nan, kungiyar ta yanke shawarar kawo karshen lokacin tsagaita bude wuta da aka shafe watanni 3 ana yi.
A ran nan, kungiyar MEND ta bayar da sanarwar ta hanyar aika wasikar email, kuma kungiyar ta yanke shawarar cewa, tun daga karfe 12 na dare na ran 16 ga wata, za a sake gudanar da aikin kai farmaki ga na'urorin man fetur da sojojin gwamnatin kasar, amma a cikin sanarwar, ba a shaida cewar ko kungiyar ta riga ta kai farmaki ga wadannan wurare ba.
Ya zuwa yanzu, a game da wannan sanarwa, gwamnatin Nijeriya ba ta mayar da martani ba.(Abubakar)
|