Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-05 16:14:40    
Shugaban kasar Mozambique ya alkawarta cewar idan ya ci zabe a karo na 2 ba zai gyara tsarin mulki don neman samun wa'adin aiki a karo na uku ba

cri

A ran 4 ga wata, shugaban kasar Mozambique Armando Emilio Guebuza ya bayyana cewa, idan ya yi nasara a sakamakon babban zabe, ba zai nemi samun wa'adin aiki a karo na uku ta hanyar gyara tsarin mulki ba.

Bisa labarin da kamafanin dillancin labaru na kasar Mozambique ya bayar, an ce, a daidai lokacin cika shekaru 17 da kulla yarjejeniyar samun sulhu a tsakanin gwamnatin da jam'iyyar hamayya ta MNR, Armando Emilio Guebuza ya ajiye furanni a bakin kabarin mazajen jiya da ke Maputo, kuma ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, ba zai nemi samun wa'adin aiki a karo na uku ba.

A kwanan baya, wasu kafofin watsa labaru na kasar sun bayar da labarin cewa, idan jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasa wato LFM ta samu kujeru kashi 2 cikin kashi 3 na majalisar dokokin, jam'iyyar za ta gyara tsarin mulki, don canja wani sashi a game da wa'adin shugaban kasar.

Kungiyar Tarayyar Turai za ta aika 'yan kallo 100 zuwa kasar Mozambique don duba zaben shugaban kasar da zaben majalisar dokoki da za a shirya a ran 28 ga wata. Daga cikinsu, a ran 4 ga wata,'yan kallo 24 sun zuwa larduna 11 na kasar Mozambique don fara aiki, kuma sauran 'yan kallo 76 za su isa yankuna a kafin za a fara babban zabe.A gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran 4 ga wata, a birnin Maputo, shugabar tawagar duba babban zaben Mozambique na kungiyar tarayyar Turai Fiona Hall ta bayyana cewa, wadannan 'yan kallo 100 sun zo daga kasashe 23 masu membobin kungiyar da kasashen Switzerland da Norway da Canada, kuma daga cikinsu a kawai jakadun kasashen membobin kungiyar Tarayyar Turai da ke a birnin Maputo.(Abubakar)