Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-16 16:26:45    
Afirka ta Kudu za ta sami tikitocin kallon gasar cin kofin duniya dubu 120 ba tare da biyan kudi ba

cri
Ran 14 ga wata, a birnin Johannesburg, hedkwatar kasar Afirka ta Kudu, an yi bikin murnar rage sauran kwanaki 300 da bude gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya wato World Cup a Afirka ta Kudu a shekarar 2010. A wannan rana, Danny Jordaan, babban darektan gudanarwa na kwamitin shirya gasar ya sanar da cewa, hadaddiyar hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta kasa da kasa wato FIFA za ta baiwa mutanen Afirka ta Kudu tikitocin kallon gasar cin kofin duniya dubu 120 ba tare da biyan kudi ba.

An labarta cewa, ma'aikata 'yan Afirka ta Kudu da suka gina filayen wasa na gasar cin kofin duniya da sauran muhimman ayyuka za su samu tikitocin dubu 40 a sakamakon gudummawar da suka bayar wajen shirya gasar cin kofin duniya. Sauran tikitocin dubu 80 kuma, kamfanoni 6 da suka ba da kudi domin shirya gasar za su rarraba su a fannonin kiwon lafiya da ba da ilmi.(Tasallah)