Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-08 20:27:12    
Kwamitin wasannin Olympic na duniya ya nuna yabo ga abubuwan tarihi da gasar wasannin Olympic ta Beijing ta haifu

cri

Yau ranar cika shekara guda da aka bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya bayar da sanarwa cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing tana da muhimmiyar ma'ana, ta haifi abubuwan tarihi da yawa.

Sanarwar ta ce, kamar yadda shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya Jacques Rogge ya bayyana a yayin da aka kawo karshen gasar wasannin Olympic ta Beijing cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing gasar wasannin Olympic ce da ba safai a kan ga irinta ba a tarihi, ta kafa sabon tarihi a fannoni da yawa, kamarsu yawan kasashe mahalartan gasar da yawan kasashen da suka samu lambobin yabo a cikin gasar da kuma tsawon lokacin talibijin na duniya da suka gabatar da wannan gasa da dai sauransu.

Dadin dadawa, sanarwar ta ce, gasar wasannin Olympic ta kalubalanci birnin Beijing wajen kyautata zirga-zirga da ingancin iska, haka kuma birnin Beijing ya kafa karin manyan ayyuka maras shinge, kana an samu karin mutanen da suka shiga aikin sa kai. Bugu da kari, an yi amfani da dakunan yin wasanni sosai. Ban da wadannan kuma, gwamnatin kasar Sin tana nuna goyon baya ga jama'ar kasar da su kara motsa jiki.(Lami)