Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-07 12:05:36    
An kaddamar da bukin nunin hotunan Beijing da na gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008 a kasar Mauritius

cri
A daidai wannan lokaci na cika shekara guda da shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekara ta 2008, a ranar 6 ga wata, a dakin adana kayayyakin tarihi da na halittu dake cibiyar Port Louis, hedkwatar kasar Mauritius, cibiyar al'adun kasar Sin dake Mauritius da kwamitin zartarwa na dakin adana kayayyakin tarihi na kasar sun kaddamar da bukin nunin hotunan Beijing da na gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008.

Jadakar kasar Sin dake Mauritius Madam Bian Yanhua, da ministan kula da harkokin matasa da motsa jiki na Mauritius Hon Satyaprakash Ritoo da dai sauran manyan jami'an gwamnatin kasar, da tawagogin 'yan diflomasiyya na kasashen waje dake kasar, gami da wakilai daga bangarori daban-daban a Mauritius sama da 60 sun halarci bukin kaddamar da nunin.

A nata bangare, jakada Bian Yanhua ta bayyana cewa, an cimma dimbin nasarori yayin da kasashen Sin da Mauritius ke inganta mu'amala da hadin-gwiwa a harkokin motsa jiki, tana fatan kasashen biyu za su ci gaba da karfafa hadin-gwiwarsu ta wannan fanni, a wani kokarin zurfafa dangantakar abokantaka tsakanin jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare kuma, a cikin jawabin da ya gabatar, Hon Satyaprakash Ritoo ya nuna babban yabo ga shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing tare da cikakkiyar nasara, haka kuma yana fatan za'a ci gaba inganta mu'amala da hadin-gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Mauritius a fannin motsa jiki.(Murtala)