Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-03 10:38:47    
Kasar Sin na ganin cewa, an cimma sakamako mai kyau a taron kolin kasashen G20

cri

An yi taron koli karo na biyu kan harkokin tattalin arziki tsakanin shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki guda ashirin a ranar 2 ga wata a birnin London na kasar Birtaniya. Mai magana da yawun kungiyar wakilan kasar Sin wanda ya halarci taron, Mista Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kasar Sin tana ganin cewa, a yayin taron kolin, an cimma matsaya a kan matakan da za'a dauka domin magance rikcin hada-hadar kudi a duniya, da yadda za'a yi domin farfado da tattalin arzikin duniya. Taron kolin ya aika da wata kyakkyawar alama ga dukkanin duniya.

Mista Ma ya ce, taron kolin ya yi alkawarin inganta manufofin tattalin arziki daga dukkan fannoni, a wani kokarin farfado da tattalin arzikin duniya, da tsaida kuduri na karfafa ikon kasashe masu tasowa na bada shawarwari. Taron kolin ya kuma cimma matsaya a kan batun inganta hadin-gwiwa a tsakanin kasa da kasa a fannin sa ido kan harkokin tattalin arziki, wanda ke shafar dukkan muhimman kafofin hada-hadar kudi da kasuwanni. Kazalika kuma, taron kolin ya sake nanata tsayawa tsayin daka kan kauracewa ra'ayin bada kariya ga harkokin ciniki, da kammala shawarwarin Doha tun da wuri. A waje guda kuma, taron ya jaddada cewa, ya kamata a mayar da hankali sosai kan harkokin neman bunkasuwa, da ci gaba da nuna goyon-baya ga gudanar da shirin bunkasa kasa na sabon karni. Wadannan nasarorin da aka cimmawa a yayin taron kolin suna da babbar ma'ana a fannonin farfado da imanin bangarori daban-daban, da tabbatar da dorewar kafofin hada-hadar kudi, gami da taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya.(Murtala)