Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-31 20:57:11    
Ministan kudi na Amurka ya nuna yabo sosai ga amfanin da Sin ke bayarwa wajen tinkarar matsalar kudi

cri

A ran 30 ga wata, a Washington, babban birnin kasar Amurka, ministan kudi na kasar Timothy Geithner ya kira karamin taron manema labarai a gabannin taron koli na kungiyar kasashe 20 wato G20 kan sha'anin kudi da za a kira a London, babban birnin kasar Birtaniya, inda ya nuna yabo sosai ga amfanin da kasar Sin ke bayarwa wajen tinkarar matsalar kudi ta duniya. Kuma yana da tabbacin cewa, akwai babbar moriya bai daya tsakanin Amurka da Sin a fannin tabbatar da tsarin kudi na duniya.

Kuma Mr. Geithner ya yi bayani ga manema labarai, cewar shugaba Obama na Amurka ya taba nuni da cewa, kulla dangantakar kut-da-kut a tsakanin Amurka da Sin a fannonin tattalin arziki da kudi na da muhimmanci sosai. Kuma ya kara da cewa, akwai babbar moriya bai daya a tsakanin kasashen biyu a fannin tabbatar da gudanar da wani tsarin kudi na duniya yadda ya kamata, kasar Sin na taka muhimmiyar taka a wannan fanni, manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa za su ba da taimako na tabbatar da tsarin kudi na duniya. Yayin da shugabannin kasashen biyu za su yi ganawa da juna a birnin London, za su yi alkawari kan ci gaba da ciyar da dangantakar da ke tsakaninsu zuwa gaba.(Kande Gao)