Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-31 16:03:56    
Shigar Sin a bankin raya kasashen nahiyar Amurka za ta inganta hadin gwiwar hada-hadar kudi tsakaninta da kasashen Latin Amurka

cri

A ran 30 ga wata a birnin Medellin na kasar Colombia, shugaban bankin tsakiya na kasar Sin Zhou Xiaochuan ya bayyana cewa, bankin raya kasashen nahiyar Amurka ya zama wani muhimmin dandali na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka, kuma shigar Sin za ta samar da dama ga bangarori biyu a fannin hadin gwiwar hada-hadar kudi.

Zhou Xiaochuan ya yi wani jawabi a matsayin memban bankin a taron ministocin kudi da shugabannin bankuna na kasashe membobin bankin raya kasashen nahiyar Amurka wato IDB a karo na 50, inda ya nuna yabo ga IDB da ya ba da taimako ga masu talauci da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a yankunan Latin Amurka da Caribbean, kuma ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da sauran kasashe membobin bankin don tinkarar rikicin hada-hadar kudi da samun bunkasuwa mai dorewa a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma a yankunan Latin Amurka da Caribbean.

A wannan rana, mashawarcin bankin raya kasa na kasar Sin Liu Kegu da shugaban bankin IDB Luis Alberto Moreno sun daddale wata takardar hadin gwiwa.

An kamala taron ministocin kudi da shugabannin bankuna na kasashe membobin bankin IDB a birnin Medellin a wannan rana, inda aka bayar da wani kuduri cewa, bankin IDB zai ci gaba da nuna goyon baya ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a yankin.(Zainab)