Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-29 21:29:06    
Kasar Amurka ba za ta nemi sauran kasashen duniya da su zuba karin jari domin raya tattalin arziki ba

cri

A ran 28 ga wata, Mr. Michael Froman, mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasar Amurka wanda ke kula da harkokin tattalin arzikin duinya a kasar ya ce, a gun taron koli na sha'anin kudi na kungiyar kasashe 20 da za a yi a makon gobe a birnin London, Mr. Barack Obama, shugaban kasar Amurka ba zai nemi sauran kasashen duniya da su kara zuba kudade domin sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki.

Amma Mr. Froman ya ce, a gun wannan taro, Mr. Barack Obama zai sake jaddada wajibi na aiwatar da shirin zuba makudan kudade domin habaka tattalin arzikin duk duniya.

Mr. Froman ya ce, shirin sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da matakan saye-saye na gwamnati na daya daga cikin muhimman batutuwan da kungiyar kasashe 20 take kulawa. Sauran muhimman batutuwan da ake kulawa su ne batun gyara tsarin sha'anin kudi da farfado da tsarin ba da rancen kudi da batun magance kariya cinikin waje da kuma batun daukar matakai domin yaduwar wannan rikicin kudi a sabbin kasuwanni da kasashe masu tasowa. Mr. Froman yana ganin cewa, kungiyar kasashe 20 ta riga ta samu ra'ayi daya kan yadda za a dauki matakan da suka wajaba wajen habaka tattalin arzikin duniya. (Sanusi Chen)