Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-26 13:41:09    
Ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar India ya shirya taron manema labaru a kan ranar cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet

cri

A ran 25 ga wata, ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar India ya shirya taron manema labaru a kan ranar cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet.

A gun taron manema labaru, jakadar kasar Sin da ke kasar India Zhang Yan ya nuna cewa, tarihi ya shaida cewa, aikin gyare-gyaren dimokuradiyya da aka yi a jihar Tibet ya kawar da tsarin manoma bayi da aka yin amfani da shi har karnuka da yawa, manoma bayi da yawansu ya wuce miliyan 1 sun sami 'yanci bayan yin gyare-gyaren, ba ma kawai shi ne muhimmin abu na tarihin bunkasuwar hakkin Dan Adam na kasar Sin, har ma wani muhimmin abu na tarihin cire tsarin manoma bayi na duniya.

Zhang Yan ya nuna cewa, Dalai Lama ba dan addini ba ne kamar yadda ya kamata, amma shi'dan siyasa ne mai gudun hijira. Ko da yake bai nuna cewar yana son ware jihar Tibet daga kasar Sin ba, amma hakikanin abu shi ne yana son ware rubu'in yanki na kasar Sin daga kasar.

Zhang Yan ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta kan nanata cewa, inda Dalai Lama ya yi watsi da aikin ware, gwamnatin kasar Sin tana son yin shawarwari tare da wakilinsa.(Abubakar)