A ran 24 ga wata, a birnin Vancouver tawagar jihar Tibet ta majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ke yin ziyara a kasar Canada ta yi shawarwari tare da jami'an asusun kula da harkokin Asiya da tekun Pacific na kasar.
A gun taron shawarwarin, Shugaban tawagar kuma mamban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma mataimakin darektan kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet mai cin gashin kanta Shingtsa Tenzinchodrak ya bayyana sakamakon da jihar Tibet ta samu a fannonin tattalin arziki da zamantakewa da al'adu da ba da ilmi da sauransu a 'yan shekaru da suka wuce, kuma ya amsa tambayoyi game da batutuwan bunkasuwar hakkin 'dan Adam da kiyaye al'adu da bunkasuwar tattalin arziki a jihar Tibet da ke jawo hankulansu.
Jami'in asusun kula da harkokin Asiya da tekun Pacific na kasar Canada ya nuna cewa, tawagar ta gabatar da sababbin bayanai game da ci gaban da jihar Tibet ta samu, kuma wannan ziyara za ta taimaka wa masu mai da hankali a kan jihar Tibet na kasar Canada wajen kara fahimtar halaccin jihar Tibet.(Abubakar)
|