Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-16 16:00:04    
Sinawa dake zama a Afrika ta kudu suna kokarin fadakar da jama'a kan bikin baje koli na duniya da za a yi a Shanghai na Sin

cri
A ran 15 ga wata, a birnin Johannesburg na Afrika ta kudu, hukumar fadakar da jama'a kan bikin baje koli na duniya na Shanghai ta Afrika ta kudu da kungiyoyin sinawa dake zama a kasar suka kafa ta wayar da kan jama'ar kasar na fannoni daban daban game da bikin baje koli na duniya da za a yi a shekarar 2010 a birnin Shanghai.

Yayin da yake ganawa da babban jami'in hukumar fadakar da jama'a kan bikin baje koli, Zhong Jianhua, jakadan Sin dake kasar Afrika ta kudu ya bayyana cewa, bisa matsayin kasar mafi girma ta tattalin arziki a Afrika, ga gwamnati da kamfannonin kasar, shiga bikin baje koli da za a yi a shekara mai zuwa tana da muhimmanci sosai. Muna fatan hukumar za ta kara mu'amala da hadin gwiwa da gwamnati da kamfannonin kasar ta yadda za su nuna karin himma wajen shiga.

Si Hai, jami'in hukumar ya ce, sinawa dake zama a Afrika ta kudu suna begen wannan biki sosai, kuma suna fatan ba da gudummowa kan wannan.(Asabe)