Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-06 14:09:00    
Sabbin ministoci guda 9 na kasar Uganda sun yi rantsuwar kama aiki

cri
A ran 5 ga wata, a fadar shugaban kasar Uganda, sabbin ministoci guda 9 da aka nada a sakamakon garambawul din da gwamnatin Uganda ta yi da ministan kula da harkokin kasar sun yi rantsuwar kama aiki, ciki har da Janet Museveni, ministar kula da harkokin yankin Karamoja kuma matar shugaban kaasr.

A ran 16 ga watan da ya gabata, shugaban Uganda Yoweri Kaguta Museveni ya sanar da yin garambawul ga majalisar ministocin kasar, inda aka tube ministan kudi, da na ma'aikatar sadarwa da ministocin kula da harkokin kasar biyar daga mukamansu, kuma ministoci da ministocin kula da harkokin kasa da dama sun samu sauyin waje. Wannan ne karo na farko da ya yi garambawul bisa babban sikeli bayan da Yoweri Kaguta Museveni ya yi tazarce a farkon shekarar 2006.(Asabe)