Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 15:23:17    
Kafofin watsa labaru na kasashen duniya sun sa lura kan matakan habaka bukatu cikin gida da kyautata zaman rayuwar jama'a da kasar Sin ta dauka

cri
A ran 4 ga wata, kafofin watsa labaru na kasashen duniya sun bayar da labaru game da kaddamar da taro na 2 na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin a karo na 11, inda suka sa lura kan matakan habaka bukatu cikin gida da kyautata zaman rayuwar jama'a da kasar Sin ta dauka a karkashin halin rikicin hada-hadar kudi na duniya.

Bisa labarin da jaridar Ashahi Shinbun ta kasar Japan ta bayar, an ce, yawancin shirye-shiryen da aka samu a taron majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin sun shafi tattalin arziki. Kuma jaridar Sankei Shimbun ta kasar Japan ta ce, mihimmin aikin dake gaban kome shi ne tabbatar da samun aikin yi da kiyaye zaman lafiya na zamantakewar al'umma a karkashin rikicin hada-hadar kudi na duniya.

Jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ta bayar da wani sharhi, inda ta ce, rikicin hada-hadar kudi ya mai da muhimman tarurruka 2 na kasar Sin na shekarar bana a matsayin muhimmin abun da ya jawo hankalin duk duniya.

Gidan telebijin na CNN ya ce, batutuwan samun aikin yi da tattalin arziki da kuma zaman lafiya na zamantakewar al'umma za su kasance muhimman batutuwan da za a tattauna a taron majalisar wakilan jama'ar Sin. Za a tattauna musamman kan yadda za a tinkari rikicin hada-hadar kudi na duniya da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin Sin a taron majalisar wakilan jama'ar Sin.(Zainab)