A ran 3 ga wata, shugaban Hukumar ba da lamuni ta duniya Dominique Strauss-Kahn ya yi gargadi cewa, matsalar kudi tana lalata sakamakon da yawancin kasashen dake kudancin Sahara suka samu a fannin tattalin arziki a shekaru goma da suka wuce. Kuma yawancinsu suna bukatar tallafi.
Bugu da kari, Mista Dominique Strauss-Kahn ya ce, yanzu kasa da kasa suna yin mu'amala mafi yawa, ba wadda za ta iya kaucewa matsalar. Ban da wannan kuma, kasashen Afrika da yawa ba su farfado daga mummunan tasiri na hauhawar farashin abinci da na mai ba, sabo da haka, kasashen suna fuskantar hali mafi tsamari.
Dadin dadawa, ya kiyasta cewa, kasashen Afrika za su bukaci karin jari daga hukumar ba da lamuni ta duniya. Kasashe 22 dake samun albashi kalilan ciki har da kasashen Afrika da yawa da suke shan fama da matsalar kudi. Ya kamata kasa da kasa za su ba da tallafin kudi na gaggawa a kalla dala biliyan 25 ga wadannan kasashe a bana don taimak musu.(Asabe)
|