Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-04 20:00:52    
'Yan sanda na Pakistan sun cafke mutane 3 wadanda ake zarginsu da laifin kai hari ga kungiyar 'yan wasan kwallon kurket ta kasar Sri Lanka

cri

A ran 4 ga wata, 'yan sanda na Pakistan sun furta cewa, bayan da suka yi aikin bincike, sun cafke mutane 3 wadanda ake zarginsu da laifin kai hari ga kungiyar 'yan wasan kwallon kurket ta kasar Sri Lanka.

Shugaban hukumar 'yan sanda ta birnin Lahore dake gabashin kasar Pakistan ya ce, wadannan mutane 3 da aka cafke sun ba da taimako ga dakarun da suke kai wannan harin ta'addanci. 'Yan sanda sun fara aikin bankado mutanen dake da nasaba da wannan lamari, ana sa ran cewa, za su samu sakamako a nan gaba ba da dadewa ba.

A ran 3 ga wata a birnin Lahore, an kai hari ga kungiyar 'yan wasan kwallon kurket ta kasar Sri Lanka wadda ke halartar wata gasar da aka yi a kasar Pakistan, inda mutane 7 suka rasa rayukansu, a yayin da 'yan wasa 6 na kasar Sri Lanka suka ji rauni. Bayan labarin, kasashen Pakistan da Sri Lanka dukkansu sun yi Allah wadai da kai harin, ministan harkokin waje na kasar Sri Lanka ya isa kasar Pakistan a ran 4 ga wata don tattauna batun harin ta'addanci da kuma aikin yanke hukunci kan lamarin.(Lami)