Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-04 14:57:11    
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun sa lura kan kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin

cri
An kaddamar da zama na biyu na taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin a karo na 11 a ran 3 ga wata a birnin Beijing. A karkashin halin rikicin hada-hadar kudi na duniya, kafofin watsa labaru na kasashen waje sun bayar da labaru da yawa game da taron, musamman a kan matakan da kasar Sin ta kauka na sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da kiyaye zaman karko na zamantakewar al'umma.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na AP ya bayar a ran 3 ga wata, an ce, wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta kira muhimman taruruka 2 bayan da rikicin hada-hadar kudi na duniya ya faru a shekarar bara, sabo da haka, an jawo hankulan kasa da kasa kan yadda za a gabatar da matakan sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce, tattalin arziki da kiyaye zaman karko a kasar Sin muhimman batutuwa ne da za a tattauna a gun muhimman taruruka 2.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ya ce, za a dora muhimmanci kan yadda za a gudanar da shirin sa kaimi ga farfado da tattalin arziki na kudin Sin Yuan biliyan 4000 a muhimman taruruka 2 na kasar Sin don cimma burin farfado da tattalin arziki da kiyaye zaman karko a kasar.

Kamfanin dillancin labaru na Kyodo ya ce, shekarar 2009 shekarar ce ta cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin, kuma kiyaye bunkasuwar tattalin arziki da zaman karko a kasar Sin su ne muhimman ayyuka na kasar Sin.(Zainab)