Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-03 20:46:58    
Wanda ya sami lambar yabo ta Pulitzer yana ganin cewa, tarurruka 2 na kasar Sin za su mai da hankali kan matsalar duniya

cri
A kwanan baya, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a kasar Nijeriya, Dele Olojede, shahararren dan jarida na Nijeriya, wanda kuma ya sami lambar yabo ta Pulitzer ya bayyana cewa, tarurruka 2 na shekara-shekara na majalisun CPPCC da NPC na kasar Sin za su mai da hankali kan matsalar hada-hadar kudi da kuma gabatar da matakan tinkarar matsalar filla-filla.

Mr. Olojede ya nuna cewa, a halin yanzu da matsalar kudi ta ratsa duk duniya, a shekarar bana, tilas ne mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC da wakilan jama'ar kasar Sin su ba da shawara kan yadda za a habaka bukatu a gida da kuma kara tsara matakai filla-filla.

Mr. Olojede ya taba zama wakilin jaridar Newsday ta kasar Amurka a kasar Sin daga shekarar 1996 zuwa shekarar 1999. A ganinsa, kasar Sin ta sami sauye-sauye ne a daidai wannan lokaci. Sinawa suna kokarin tabbatar da manufar raya kasa ta zamani bisa karfin aniya. Ya ce, "Na kan gaya wa abokaina 'yan Nijeriya cewar, jama'ar Nijeriya na bukatar irin wannan aniyar da Sinawa suke da ita domin kyautata halin da kasarsu ke ciki. A kasar Sin, manoma da 'yan ci rani da kuma wadanda ke aiki a ofis dukkansu suna aiki tukuru a ko wace rana. "(Tasallah)