Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-27 11:06:41    
Kungiyoyin Palesdinu sun yi alkawarin yin kokari wajen samun sulhuntawa tsakanin kabilu

cri
A ran 26 ga wata, kungiyoyin Palesdinu masu halartar shawarwarin sulhuntawa sun cimma daidaito a brinin Alkahira na kasar Masar, kuma sun yi alkawarin daukar hakikanin matakai don kawar da bambanci tsakanin al'ummomin Palesdinu da samun sulhuntawa.

A cikin sanarwar da aka bayar bayan shawarwarin, kungiyoyin sun tsai da kafa kwamitocin aiki guda 5 don kula da batutuwan da suka shafi sulhuntawa tsakanin kabilun Palesdinu, a ciki har da batun kafa gwamnatin hadin gwiwa da sauran muhimman batutuwa. Kwamitocin za su fara aiki tun daga ran 10 ga watan Maris, kuma ana sa ran cewa, za su kammala aiki a karshen watan Maris.

Hakazalika masu halartar shawarwarin sun yarda da kafa wani kwamitin da ya hada da wakilan kasar Masar da na kungiyar tarayyar kasashen Larabawa don daidaita bambancin da ke tsakanin kwamitocin 5 idan aka bukata.(Zainab)