Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-20 13:50:18    
Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya nuna cewar dangantakar tsakanin Sin da kasashen kudancin Amurka ta samu ci gaba sosai

cri

A ran 19 ga wata, a birnin Brasilia, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi da ke yin ziyarar kasar Brazil ya nuna cewa, a 'yan shekaru baya, dangantakar tsakanin Sin da kudancin Amurka ta samu ci gaba sosai, kuma tana da makoma mai kyau.

A gun taron manema labaru da aka shirya a ran nan bayan Yang Jiechi ya yi shawarwari tare da ministan harkokin waje na kasar Brazil Celso Amorim, Yang Jiechi ya nuna cewa, kasar Sin tana mai da hankali a kan dangantakar da ke tsakanin Sin da  kudancin  Amurka da yankunan Carribean sosai.

A 'yan shekaru baya, dangantakar tsakanin bangarorin biyu ta samu bunkasuwar sosai, bangarorin biyu suna kara kai ziyara ga juna, kuma sun sa kaimi ga yin hadin gwiwar tattalin arziki a fanonnin daban daban da kara habaka ma'amala, kuma sun kara shiga yin musanyar ra'ayoyinsu da yin hadin gwiwa a batutuwan duniya. A ganinsa, a karni na 21,  kudancin  Amurka da yankunan Carribean za su taka muhimiyyar rawa a harkokin siyasa da tattalin arziki da al'adu na duniya.

Yang Jiechi ya yi yabo ga yunkurin dunkulen tattalin arzikin kudancin Amurka da yankunan Carribean bai daya, kuma ya yi babban yabo ga muhimmiyar rawa da kasar Brazil ta taka. Ya ce, a bana ne aka cika shekara 35 da kasar Sin ta kafa huldar diplomasiya tare da Brazil, a cikin shekaru 35 da suka wce, dangantakar tsakanin Sin da Brazil ta samu ci gaba sosai, a ganinsa, dangantakar tana da makoma mai kyau.(Abubakar)