Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-18 17:23:48    
Hadin gwiwar Sin da Afirka na da kyakkyawar makoma, a cewar Yang Jiechi

cri
A ran 17 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi da ke yin ziyarar aiki a kasar Afirka ta Kudu ta yi bayani a birnin Johannesburg, cewar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka za ta samu wata sabuwar dama wajen samun bunkasuwa a shekara ta 2009, bangaren Sin zai ci gaba da sa kaimi ga hadin gwiwar bangarorin biyu, musamman ma inganta hadin gwiwarsu a hakikanan fannoni.

Lokacin da yake zantawa da manema labarai, Mr. Yang ya bayyana cewa, inganta dangantakar hadin gwiwa ta aminci tsakanin Sin da Afirka wani muhimmin tushe ne na manufofin kasar Sin a fannin diplomasiyya, haka kuma ita zaba ce da bangaren Sin ya yi cikin dogon lokaci bisa manyan tsare-tsare. A shekarar da ta gabata, bangarorin Sin da Afirka sun yi cudanya sosai tsakanin manyan matakai, da kuma karfafa amincewar juna bisa manyan tsare-tsare. Haka kuma Sin da Afirka suna ta inganta hada kansu a fannoni daban daban, wanda ya kawo musu alheri a zo a gani. A cikin wannan sabuwar shekara, kasar Sin za ta inganta hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannonin raya muhimman ayyukan yau da kullum da ayyukan gona da sadarwa da raya 'yan kwadago da dai sauransu, ta yadda za a kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka.(Kande Gao)